Hukumar zaben Nijar na shirye-shiryen zabukan da ke tafe

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar a yau hukumar zabe mai zaman kanta CENI a takaice , ta bude wani zaman bada horo ga mambobinta na jihohi da kananan hukumomin kasar baki daya.

Manufar wannan horo dai ita ce baiwa mambobin hukumar zaben cikakkun bayanai a kan gudanar da zabukan dake tafe tare da kauce wa samun kura-kuran da ka iya haddasa cikas ga zabukan.

A ranar 8 ga watan mai tsayawa ne dai za a yi zabukan kananan Hukumomi a Nijar din, yayinda kuma za'a gudanar da tagwayen zabukan shugaban kasa zagaye na farko da na 'yan majalisar dokoki na kasa a ranar 31 ga watan na Janairu .

Zabukan ne dai za su kai sojoji ga mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula a ranar 6 ga watan Afrilu mai zuwa.