An yankewa Khodorkovsky hukuncin dauri a jarun

Mikhail Khodorkovsky
Image caption Mikhail Khodorkovsky

Wata kotu a Rasha ta yankewa tsohon hamshakin attajirin nan na kasar, Mikhail Khodorkovsky hukuncin daurin shekaru 14 a gidan kaso bisa laifin almundahana da halatta kudaden haram.

Hukuncin ya hada da wanda aka yanke ma shi a baya bisa kaucewa biyan haraji, wanda hakan ke nufin ya samu karin shekaru bakwai a gidan kaso kenan.

A farkon wannan makon lauyoyinsa sun nuna alamun za su daukaka kara kan duk wasu karin shekaru da za'a yanke ma shi.

Kasashen yammaci dai sun yi ta sukar yadda aka gudanar da shari'ar Mr Khodorkovsky, wanda ya dade yana adawa da pira ministan Rashan, Vladimir Putin.