Ambaliyar ruwa a wasu sassan Austuraliya

Ambaliyar ruwa a wasu sassan Australiya
Image caption Ambaliyar ruwa a wasu sassan Australiya

Koguna a jahar Queensland dake arewa maso gabashin Australiya, na ci gaba da tumbatsa, inda wani bangare na jahar ke fuskantar ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba cikin sama da shekaru hamsin.

Waklin BBC yace kawo yanzu ruwan ya sha kan garuruwa ashirin da biyu a jahar Queensland, abinda ya tilasta wa dubban mutane ficewa daga gidajensu, tare kuma da lalata wuraren kasuwanci.

Yanzu haka ana amfani da jiragen sojoji wajen jefa kayayyaki ga mutanen dake wuraren da lamarin ya fi shafa.

Ana ganin bala'in ambaliyar ruwan ya jawo asarar biliyoyin daloli a jahar.