Shugaba Jonathan zai ziyarci kasar Benin

Ana sa ran a yau shugaban Nijeriya, Dr Goodluck Jonathan zai je jamhuriyar Benin domin tattaunawa da takwaran aikinsa, Bani Yayi, game da rikicin siyasar kasar Kotde Vuwa.

Shugaban kasar na Benin, Boni Yayi, na daga cikin shugabannin kasashen Afirka ta yamma uku na kungiyar ECOWAS, da suka je Kotde Vuwa, a farkon wannan makon, inda suka gaza shawo kan shugaba mai ci Laurent Gbagbo da ya sauka daga mulki.

Majalisar Dinkin Duniya, da ma wasu kungiyoyi sun ce Mr. Gbagbo ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Nuwambar da ya gabata, zaben da abokin hamayyarsa Alassane Watara yayi nasara.