An yi ma wani yaro kisan gilla a Kebbi.

'Yan sanda a jihar Kebbi Najeriya sun ce sun soma bincike kan kisan gillar da aka yi wa wani yaro mai shekaru uku a garin Yauri da ke kudancin jihar.

An dai samu gawar Aliyu Kabir a cikin wani gidan da ba a kamalla gininsa ba, ba tare da wasu sassan jikin ba, kwana daya bayan da iyayensa suka sanar da bacewarsa.

'Yan sanda na rokon duk wasu masu bayanai da zasu kai ga cafke wadanda suka aikata kisan, da su bada hadin kai.

Kashe kashe irin wannan dai ana danganta su da masu yin tsafi, domin biyan wata bukata, ko dai ta siyasa, ko ta yin kudi dare daya.