Yakin neman zaben shugabannin kananan hukumomi a Nijar

Tutar Jamhuriyar Nijar
Image caption Za'a soma yakin neman zaben shugabannin kananan hukumomi a Nijar

A Jamhuriyar Nijar za'a soma farfagandar zaben kananan hukumomin da za'a yi ranar 8 ga watam janairun shekarar 2011

Sama da Kansiloli 3000 ne za'a zaba cikin kananan hukumomi 266 a fadin kasar baki daya.

A cikin jawabin kaddamar da farfagandar da yayi a jiya, shugaban mulkin sojin Nijar Janar Salu Djibo, yayi kira da 'yan kasar dasu fito yadda ya kamata a ranar zaben domin ganin cewar sun zabi wakilansu da za su tafiyar da ayyukan cigabansu.

Sannan kuma shugabankasar ta Nijar yayi kira ga Shugabannin hukumar zabe ta CENI, da suyi aikinsu tsakani da Allah