'Yan Kasar Zimbabwe a kasar Afirka ta Kudu

Taswirar kasar Afirka ta Kudu
Image caption Afirka ta Kudu na yiwa dubun dubatar 'yan ciranin kasar Zimbabwe dake rayuwa a Afirka ta Kudu rajistar zama a kasar.

Dubun dubatar 'yan ciranin kasar Zimbabwe dake zaune a Kasar Afirka ta kudu na yin layi a wajen ofisoshin gwamanti, domin a yi masu rajistar zama a kasar kafin wa'adin da aka deba masu ya cika a yau.

Idan har basu sami iznin zama ba a kasar, to kuwa za'a tusa keyarsu zuwa gida.

Ministar kula da al'amuran cikin gida ta Afirka ta kudu Nkosazane Dlamini Zuma tace da zarar an kammala wannan aiki, za'a tusa keyar duk wanda aka kama ya tsallako kan iyakar kasar ba tare da takaddar iznin shigowa ba

Ana tunanin 'yan kasar Zimbabwe dake rayuwa a Afirka ta Kudun, zasu kai mutum miliyan biyu, amma sai dai wadanda ke da izinin zama cikinsu basu wuce mutum dubu dari da arba'in ba