An rantasar da Dilma Rouself a matsayin shugabar Brazil.

brazil
Image caption Shugaba Dilma Rouself ta Brazil

An rantasar da sabuwar shugabar kasar Brazil Dilma Rouself.

Madam Dilma wacce tsohuwar yar gwargwarmaya ce a jammiyar masu ra'ayin rikau ta fuskanci azabtarwa a zamanin mulkin soja.

Kuma ita ce mace ta farko da zata ja ragamar mulkin Brazil,wadda ita ce kasar data fi sauran kasashen dake yankin Latin Amurka yawan alumma

Bayan da aka rantar da ita a jawabin da ta gabatar shugabar Brazil din Dilma Rouself ta yi alkawarin kare kundin tsarin mulkin kasar tare da yin biyaya ga dokokin kasar.