Bom ya hallaka mutane 7 a wata Majama'a a Masar

Taswirar Alexandria dake Masar
Image caption Wani bam daya fashe a wajen wata majama'a a kasar Masar yayi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai da kuma jikkata fiye da mutane ashirin

Wani bam ya fashe cikin wata mota a wajen wata majama'a dake garin Alexandria a arewacin kasar Masar.

Mutane bakwai ne suka mutu. Sama da mutum ashirin kuma sun sami raunuka.

Bam din ya fashe ne a lokacinda masu ziyarar ibadah suka bar majama'ar, bayan an gudanar da adduo'in murnar shiga sabuwar shekara.

Motocin daukar marasa lafiya sun kwashi wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin dake wannan yankin

Wakiliyar BBC tace bayan da aka kai harin, rahotanni sun ce sai daruruwan kiristoci suka fito kan tituna suna kokarin kai hari akan masallatai