Estonia ta fara amfani da kudin Euro

Estonia zata fara amfani da kudin Euro
Image caption Kasar Estonia ta shiga sabuwar shekara tare da canjin kudinta zuwa kudin Euro

Al'ummar kasar Estonia sun shiga sabuwar shekara tare da yin canjin kudinsu zuwa kudin Euro.

Bankuna da na'urorin komputa sunyi ta shirye shirye na aiwatar da wannan canji daga tsohon kudin kasar na Estonia Kroon.

Estoniyawa dai 'yan tsirarune a cikin al'ummar nahiyar turai.

Masu sharhi sunce shawarar da kasar ta dauka na fara amfani da kudin Euro a wani lokaci na rikici a nahiyar turan, zaisa kudin Euron yayi bunkasar da ba'a bukata