Ba zan bada mulkin ba- Shugaba Gbagbo

Shugaba Laurent Gbagbo
Image caption Shugaba Laurent Gbagbo ya sake nanata cewar ba zai bada mulkin kasar ba don kuwa shine ya lashe zaben a cewarsa

A wani jawabin da yayi na murnar shiga sabuwar shekara, shugabankasar Ivory Coast Laurent Gbagbo wanda yaki amincewa ya sauka daga kan kujerar mulki, ya nanata cewar ba zai bada mulkin ba.

Shugaban ya kuma zargi kasashen duniya da kokarin yi masa juyin mulki.

Ya kuma yi kira ga abokin hamyyarsa Alassane Ouattara, daya zo su zauna domin su tattauna

Mr Gbagbo yace 'yan kasar Ivory Coast ne suka sake zabensa. saboda haka ba zai bada mulki ba.

Ya kara da cewar tsarin mulkin kasar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta sun bayyana cewar abokin takarar tasa ya fadi zabe