An fara asarar rai a ambaliyar Australia

Ambaliyar ruwa a Queensland
Image caption Ambaliyar ruwa a Queensland

Ambaliyar ruwan da ta mamaye yankuna da dama na jihar Queensland da ke Australia ta hallaka wata mata.

Matar ta nutse ne a arewacin jihar bayanda ruwa ya ture motar da take tukawa. 'Yan sanda kuma na cigaba da neman wasu mutane da suka bace sanadiyyar ambaliyar.

Kodayake ruwan ya fara ja da baya a wasu sassan, dubunnan mazauna jihar Queensland ne suka kauracewa gidajensu.

Kevin Martin ya bar gidansa ranar Juma'a amma ya koma a kwale-kwale don ganin halin da ya ke ciki.

Yace; "Na zo ne in tabbatar komai na nan kuma babu wanda ya wawashe ni, shi ne dai abinda ya fi damu na."

Yanzu haka dai garuruwa ashirin ne ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan da ya mamaye yankin da ya kai fadin kasashen Jamus da Faransa a hade.