Soji ne kawai za su iya sauke Gbagbo - Soro

Gbagbo da Ouattara
Image caption Gbagbo da Ouattara

Wani na hannun daman Alassane Ouattara, mutumin da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin halattaccen shugaban kasar Ivory Coast, ya ce shugaba mai ci Laurent Gbagbo ba zai taba sauka daga mulki ba sai an yi amfani da karfin soji.

GIYOM SORO, wanda Mr. Ouattara ya nada firaminista ya yi kira ga kasashen duniya da su yi amfani da karfin da ya dace wurin tumbuke Mr. Gbagbo daga kujerar mulki.

A baya dai, shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi alkawarin cewa kungiyar kawancen kasashen yammacin Afrika, ECOWAS za ta yanke mataki na gaba da za ta dauka kan rikicin da ke cigaba a Ivory Coast a mako mai kamawa.

Tuni dai ECOWAS din ta tura shugabannin Afrika har uku zuwa Ivory Coast domin shawo kan Mr. Gbagbo ya sauka daga mulki yayinda wani jami'in majalisar dinkin duniya ya yi gargadin cewa kalaman da ke fitowa daga shugabannin siyasar kasar za su iya rura wutar rikicin.