'Yan fashi sun kama jirgin ruwan Algeria

Dan fashi a gabar teku
Image caption fashin jirgin ruwa a Somalia

'Yan fashi sun kama wani jirgin ruwan kaya na Algeria tare da matukansa ashirin da bakwai a daura da gabar kasar Oman.

Jirgin ruwan mai suna Bilda, mai daukar ton dubu ashirin da shida ya fada hannun 'yan fashin ne kan hanyarsa ta zuwa Darus Salam a Tanzania.

Matukan jirgin sun hada da 'yan kasashen Algeria, da Tanzania, da kuma Philippines.

Kafin wannan jirgin dai wasu masu fashin jirgin 'yan kasar Somalia sun kame wani jirgin ruwan Mozambique kimanin kilomita dari daga tsibirin Comoros.

Rundunar yaki da fashin jiragen ruwa ta Tarayyar Turai ta ce masu fashin jirgi a yankin na tsare da jiragen ruwa ashirin da takwas tare da ma'aikatansu fiye da dari shida da hamsin a yanzu haka.