'Boko Haram' sun hallaka dan sanda a Najeriya

Jami'an 'yan sandan Najeriya
Image caption An hallaka wani dan sanda

An bindige wani dan sanda har lahira a Maiduguri babban birnin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Jami'ai sun dora alhakin kisan akan haramtacciyar kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ake zargi da jerin wasu hare-hare a baya bayan nan.

An hallaka dan sandan ne a safiyar yau, a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida daga aikin kwana da ya yi a birnin na Maidugurin, inda kungiyar ta dauki alhakin kai wasu jerin- hare hare akan wasu coci coci.

A yanzu dai jami'ai suna shawartar 'yan sandan da su guji sanya kayansu na aiki, idan dai ba'a bakin aikin su ke ba.