Rijistar zaben raba-gardama a Sudan

Tutar Kudancin Sudan

Kimanin mutane miliyan hudu ne suka yi rajista domin shiga zaben raba gardama na samun 'yancin kan yankin Kudancin Sudan, wanda aka shirya farawa ranar lahadi mai zuwa.

Wani mai magana da yawun hukumar shirya zaben raba gardama na kudancin Sudan, ya ce fiye da kashi casa'in da biyar cikin dari na mutanen da suka yi rajistar sun fito ne daga yankin kudancin kasar -- yayin da sauran kuma suka yi tasu rajistar a arewacin Sudan da kuma kasashen waje guda takwas.

Zaben raba gardamar dai wani bangare ne na ka'idojin cimma yarjejeniyar sulhu ta shekara ta 2005 da aka yi tsakanin arewacin Sudan din da kudancin ta, bayan da aka shafe fiye da shekaru ashirin ana fama da yakin basasa.

Deng Alor Kuol, minista a gwamnatin kudancin Sudan din, ya ce a gobe ne ake sa ran shugaban Sudan Omar Al-Bashir zai ziyarci kudancin Sudan din don neman hadin kai.