ECOWAS za ta cigaba da tattaunawar sulhu kan Ivory Coast

Rikicin siyasar Ivory Coast
Image caption Rikicin siyasar Ivory Coast

Shugaban Hukumar gudanarwa ta kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma, ECOWAS, James Victor- Gbeho ya ce Laurent Gbagbo ya amince a tattauna don kawo karshen rikicin siyasar da Ivory Coast ke fama da shi cikin ruwan sanyi, kuma ba tare da wasu sharudda ba.

Haka kuma, Mr Victor -Gbeho ya ce Mr Gbagbo ya yi alkawarin dage kawanyar da sojojin dake marawa ma sa baya su ka yiwa otel din da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, ke da ofisoshinsa.

Tun farko dai a karshen wani taro da ta yi a Abuja, kungiyar ta ECOWAS ta amince ta sake tura wata tawagar shugabanninta zuwa kasar don cigaba da tattaunawa da bangarorin biyu dake jayyaya da juna.

Hakan ya biyo bayan gazawar wata tawagar shugabanni da kungiyar ta ECOWAS ta tura kasar ne tun farko wajen shawo kan shugaba Laurent Gbagbo ya sauka daga mulki.

A baya dai kungiyar ECOWAS ta sha alwashin daukar duk wani matakin da ya dace wajen tunbuke Laurent Gbagbo, ko da ta kama a yi amfani da karfin soji.