Najeriya za ta dau matakan hana tashin bom

fashewar bom a Najeriya
Image caption Fashewar bom a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta baiyana sababbin matakan tsaron da za ta dauka bayanda bama-bamai suka hallaka fiye da mutane tamanin a kasar a jajiberin Kirsimeti da kuma ranar sabuwar shekara.

Kakakin shugaban kasar Ima Niboro ya ce Mr. Goodluck Jonathan zai nada mashawarcin na musamman kan harkokin ta'addanci ya kuma kafa kwamiti na musamman da zai kula da amfani da abubuwa masu fashewa tare da fadakar da al'umma kan barazanar da suke fuskanta.

Mr. Ima Niboro ya kuma ce gwamnati za ta sanya kyamarori a wuraren taruwar al'umma tare da gaggauta kame da tuhumar mutanen da ya kira 'yan bangar siyasa.

A makon gobe ne dai jam'iyyar PDP mai mulkin kasar za ta gudanar da zabubbukan fidda gwanayen da za su tsaya mata takara a babban zaben watan Afrilu mai zuwa.