Al-Bashir zai ziyarci kudancin Sudan

Omar al-Bashir
Image caption Shugaban Sudan

Shugaban Sudan Omar al-Bashir zai ziyarci Juba, babban birnin kudancin kasar, ranar Talata, gabannin kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan yiwuwar bai wa yankin 'yancin kansa a makon gobe.

Mr. Bashir zai gana da shugaban yankin mai cin gashin kansa, Salva Kiir domin tattauna batutuwan da za su biyo baya idan har yankin ya zabi samun 'yanci kamar yadda ake hasashe.

Batutuwan sun hada da yadda za'a tafiyar da arzikin man fetur da kogunan kasar da kuma makomar 'yan kudun da ke zaune a arewacin Sudan.

Wakilin BBC James Copnall ya ce gwamnatocin Sudan dai sun jima su na nunawa kudancin kasar wariya tun daga zamanin mulkin mallaka zuwa yanzu. Haka kuma bangarorin biyu sun sha bamban ta fuskar al'ada, da addini, da kabila, da kuma yakin da suka sha yi da juna.