Shugaba al Bashir na ziyara a Juba

shugaban Sudan al- Bashir
Image caption shugaban Sudan al- Bashir

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya ce zai yi bakin ciki idan aka ce kasar ta dare gida biyu, yayin da ake daf da yin zaben referendum, wanda ake sa ran zai kai ga ba kudancin kasar 'yan cin kai.

Mr. al-Bashir na magana ne a Juba, babban birnin kudancin Sudan din, a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin din kasar:

To amma kuma Mr al Bashir ya ce za su yi farin ciki idan har hakan zai samar da zaman lafiya mai dorewa a duka bangarorin Sudan. Shugaba Omar al-Bashir ya kara da cewa zai mutunta zabin jama'a kuma ya taimaka wajen ci gaban kudancin Sudan, idan har yankin ya balle.