An yi janazar gwamnan da aka kashe a Pakistan

Janazar gwamnan da aka kashe a Pakistan
Image caption Ana bukatar sabbin matakan tsaro

Mutanen Pakistan da dama ne suka halarci jana'izar gwamnan yankin Punjab, Salmaan Taseer wanda aka gudanar dazu a birnin Lahore.

An yi masa kisan gilla ne a jiya talata.

Firaministan kasar tare da manyan 'yan siyasa sun halarci janaizar.

A daidai lokacin da ake jana'izar, wasu kuma sun gudanar da zanga-zanga a yankin Peshawar, inda suke nema a sako mutumin da ya halaka shi.

Ministan kula da tsiraru na Pakistan, Shabhaz Bhatti, wanda shi ma sananne ne, wurin yin suka ga dokokin sabo a kasar, ya shaida wa BBC cewa mutane kamarsa, sun yi imanin cewa ana yi wa wannan dokar ce hawan kawara.