Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP

Image caption Shugaban Jami'iyyar PDP Okwselieze Nwodo

A Najeriya, rikicin cikin gida wanda ke bibiyar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar a jihohi daban-daban yana ta kara zama wata gagarumar matsala, sakamakon yadda ake ta samun tayar da kayar baya da tashin-tashina dangane da zabubbukan shugabannin rassan jam'iyyar na jihohi da kananan hukumomi.

Al'amarin da wasu masu lura da al'amura ke ganin hakan yana iya shafar karfi da nasarar jam'iyyar a zaben da ke tafe.

Sai dai uwar jam'iyyar ta musanta wannan hasashe. Rahotanni daga jihohi daban-daban na Najeriya, sun nuna cewa, jam'iyyar PDP mai mulkin kasar tana da fama da matsaloli ko rigingimu irin na cikin gida, wadanda bisa ga dukkan alamu suka kara kamari a 'yan kwanakin nan. A jihar Bauchi, ga misali, wasu 'ya'yan jam'iyyar sun yi zargin cewa, an tafka magudi a zabubbukan fidda wakilai da na 'yan takarar majalisar dokoki ta jihar na jam'iyyar, zargin da shugabannin jam'iyyar kuma suka musanta.

Bangar siyasa

A jihar Nasarawa kuwa, an ce har hatsaniya wasu matasan jam'iyyar suka tayar, a sanadiyyar abin da suka kira, kakaba 'yan takara a kan 'yan jam'iyyar.

Yayin da a jihar Oyo asarar rayuka ake zargin an yi a wajen taron fidda wakilan jam'iyyar, abinda ya kai ga garkame shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan Najeriya Sanata Taslim folarin a jarum, bisa zargin kisan kai a taron jam'iyyar.

A jihar Enugu kuma, batun zaben shugabannin jam'iyyar na jihar ne ya haddasa rarrabuwar kai, a tsakanin bangaren gwamnan jihar, Baritsa Sullivan Chime da bangaren shugaban jam'iyyar na kasa, Dokta Okwesilieze Nwodo.

Sakamakon takaddamar da ta sarke game da zaben shugabannin reshen jam'iyyar na jihar, a cewar Barista Ray Nnaji wani dan bangaren gwamnan: "Zaben shugabannin da aka ce bangaren Dokta Okwesilieze Nwodo, wato shugaban jam'iyya na kasa, ya gudanar ya saba doka, kuma bata lokaci ne kawai. Domin mu ba mu amince da zaben ba."

Shi kuwa bangaren shugaban jam'iyyar PDP na kasa, yana ganin ba haka abin yake ba, a cewar Mista Harrison Ogara, sabon sakataren yada labaran jam'iyyar a jihar Enugu: "Ai 'yan bangagren gwamnan ba su da wata hujja da za su ce, zaben ya saba doka, kotu ce kawai za ta iya yanke hukunci game da haka. Suna dai maganganu ne kawai marasa kan gado." Irin wannan ja-in-ja da ta dabaibaye jam'iyyar PDP a sassa daban-daban na kasar, ta sa masu lura da al'amura irin su Mista Emmanuel Nzomiwu suna bayyana fargaba game da makomar jam'iyyar: "An tasar wa ruguza jam'iyyar, ba wai a sakamakon fafutukar masu adawa da ita daga waje ba, amma sakamakon rigingimun cikin gida. Kuma hakan na iya tadiye nasarar da jam'iyyar za ta samu a zabubbukan da ke tafe. Saboda haka, ya zama wajibi PDP ta tabbatar da tsarin dimokuradiyya a cikin gida." Sai dai wani jami'in jam'iyyar PDP na kasa da wakilin BBC ya tuntuba ta wayar taho, wanda kuma bai so a ambaci sunansa ba, ya yi watsi da irin wannan fargaba da ake bayyanawa. A cewarsa, ana kokarin shawo kan matsalolin da suka taso a jam'iyyar.