Prince Tony Momoh ya zama sabon shugaban CPC

Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin kasa a CPC
Image caption Wakilan jam'iyyar CPC sun kammala zabubbukan shugabannin jam'iyyarsu bayan da suka shafe kwanaki biyu suna zaben

A Najeriya jam'iyyar adawa ta CPC ta zabi sababbin shugabannin da za su jagoran-ce ta bayan wakilan jam'iyyar wato deleget-deleget sun shafe kwanaki biyu suna zaben shugabannin.

Sabon shugaban jam'iyyar dai shi ne Prince Tony Mommoh wanda ya fito daga shiyyar kudu-maso-kudancin Najeriya.

Prince Tony Momoh dai ya taba rike mukamin ministan yada labaru a lokacin gwamnatin mulkin sojin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Sauran wadanda aka zaba a mukamai daban daban na jam'iyyar ta CPC sun hada da mataimakan shugaban jami'iyyyar da kuma sakataren kudi da dai sauransu.

Eng. Buba Galadima shi ne mutumin da aka zaba a matsayin sakataren jam'iyya na kasa babu hamayya.