Takaitaccen tarihin marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

Image caption Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

A lokacin rayuwarsa, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya kasance masanin tarihi, tsohon soja, dan siyasa, kuma mutumin da aka fi sani a matsayin wanda ya jagoranci yunkurin ballewar yankin kudu maso gabashin Najeriya da nufin kafa jamhuriyar Biafra, wato yunkurin da bai ci nasara ba. An haifi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ne a ran hudu ga watan Nuwamban shekarar 1933, a garin Zungeru na jihar Naija a arewacin Najeriya.

Ko da yake mahaifinsa, Sir Louis Odumegwu Ojukwu dan asalin garin Nnewi na jihar Anambra ta kudu maso gabashin kasar ne, wanda ya yi fice kuma ya kudance a harakar sufuri. Emeka, kamar yadda akan kira shi a takaice, ya fara karatunsa na boko ne a birnin Ikko, kuma tun yana dan shekara goma sha uku mahifinsa ya tura shi kasar Birtaniya, inda ya yi karatun digiri na farko a fannin tarihi, daga bisani kuma ya sake komawa ya yi digiri na biyu a wannan fanni.

Marigayin ya fara aikin gwamnati ne karkashin Turawan mulkin mallaka a matsayin jami'in mulki na yankin Udi a tsohuwar jihar Gabas.

Sai dai bayan 'yan watanni, ya bar wannan aiki ya shiga soja, a shekarar 1957. Inda ya rike mukamai da dama, wadanda suka hada da Kwata masta Janar, da kula da bataliya ta biyar ta sojan Najeriya da ke Kano.

Kana ya zama gwamnan mulkin soja na tsohuwar shiyyar gabas, bayan da Janar Aguyi-Ironsi ya karbi ragamar shugabancin Najeriya a shekarar alif da dari tara da sittin da shida. Marigayi Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, wanda ya kai mukamin laftanar kanar a aikin soja, ya jagoranci yunkurin ballewar shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, da nufin kafa jamhuriyyar Biafra, a shekarar alif da dari tara da sittin da bakwai. Wannan al'amari ya haddasa yakin basasa a Najeriya na tsawon watanni talatin, tare da asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa. Sai dai dab da karshen yakin, Ojukwu ya yi gudun hijira zuwa kasar Ivory Coast a shekarar alif da dari tara da saba'in.

Kuma bayan kwashe tsawon shekaru goma sha uku a waccan kasa, gwamnatin Alhaji Shehu Shagari ta yi wa tsohon madugun 'yan tawayen afuwa, ya dawo gida Najeriya a shekarar alif da dari tara da tamanin da biyu.