Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yarjejeniyar CPC da ACN ba za ta yi nasara ba - Naja'atu

Image caption A baya Hajiya Naja'atu Muhammad na daga cikin na hannun damar janar Buhari

Wata kusa a jam'iyyar adawa ta ACN a Najeriya, Hajiya Naja'atu Muhammad ta ce tattaunawar da ACN ke yi da CPC domin fuskantar jam'iyyar PDP ba za ta je ko'ina ba.

Naja'atu ta danganta hakan ne da halayen son kai da tace janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar ta CPC ya dade yana nuna wa, ayunkurin da aka yi na hada kai a baya.

Yanzu haka al'amuran siyasa sun kankama a Najeriya yayinda miliyoyin 'yan kasar da suka cancanci jefa kuri'a suke shirin zabar sabbin shugabanni da wakilai a watan Afrilu mai zuwa.

Hajiya Naja'atu Mohammed, wacce ta ziyarci ofishin BBC na London, ta soki wasu akidun janar Muhammad Buhari, wanda a baya abokin tafiyar siysar ta ne.

Jamilah Tangaza ta tattauna da ita a kan abubuwa da dama da suka hada da siyasa dama rashin tsaro a Najeriya: