An soki shirin amfani da soji kan Ivory Coast

Sojojin kiyaye zaman lafiya
Image caption A yanzu haka akwai sojojin Majalisar Dinkin Duniya da dama a kasar

Shugaba John Atta Mills na Ghana ya ce bai jin yin amfani da karfin soji zai warware matsalar Ivory Coast, bayanda Laurent Gbagbo, ya ki sauka daga mukamin shugaban kasar.

Shugaban ya kuma nisanta kansa daga shawarwarin yin amfani da karfi a kasar da 'yan Ghana kusan miliyan daya suke da zama da kuma aiki.

Ya ce Ghana ba za ta nuna banbanci ba, kuma baya jin matakin soji zai samar da zaman lafiya a Ivory Coast.

Kungiyar yankin yammacin Afrika ta ECOWAS, wadda kasar Ghana wakiliya ce a cikinta, ta yi barazanar tilastawa Mr Gbagbo mika iko ga wanda aka amince ya lashe zaben watan Nuwamba, Alassane Ouattara.