Za'a binciki dalilin barkewar Kwalara a Haiti

Kasar Haiti
Image caption Kwararru zasu fara bincike dangane da musabbabin barkewar annobar kwalara a Haiti

Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya, Ban ki Moon ya nada wani kwamitin bincike wanda aka dorawa alhakin gano abun da ya janyo barkewar annobar cuttar kwalera a kasar Haiti.

Za'a baiwa Kwararun da suka fito daga kasashen Mexico, Peru , Amurka da kuma India, damar baiwa majalisar bayanai game da hakan

Kuma zasu yi tafiya zuwa kasar ta Haiti domin su gudanar da bincike a wurin.

Wakiliyar BBC ta ce ana zargin sojojin wanzar da lafiya na kasar Nepal da kawo cuttar kwalarar zuwa kasar, saboda suna zama kusa da wani kogi , inda a nan ne aka samun barkewar cutar