Ko Man fetur din Sudan zai wadatar da Kudu da Arewa?

Man fetur a Sudan
Image caption Tattalin arzikin kasar dai ya dogara ne kan man fetur

Man fetur ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban Sudan, kuma duk wanda ya ziyarci birnin Khartum, to babu shakka zai ga hakan a zahiri.

Sai dai a yanzu da Kudancin kasar ya balle bayan kuri'ar raba gardamar da aka gudanar a watan Janairu - sun tafi da yawancin arzikin man.

"Babban abin da ke jan hankali a kan ballewar Kudancin Sudan, shi ne makomar arzikin mai", a cewar Rosie Sharpe ta kungiyar Global Witness, wacce ta fitar da rahoto kan arzikin man.

"Ba tare da wata sabuwar yarjejeniya kan man tsakanin Kudanci da Arewaci ba, zai yi wuya Kudancin kasar ya balle cikin sauki."

Kimanin mutane miliyan biyu ne aka kiyasta sun mutu a shekaru 20 da aka shafe ana yakin basasa tsakanin yankunan biyu.

Amma wasu na ganin ballewar za ta haifar da makoma mai kyau ga kasashen biyu.

Dogaro kan man fetur

Tun yarjejeniyar sulhu ta shekarar 2005, Arewaci da Kudancin kasar suke raba arzikin man kai-da-kai - kuma mafi yawan ganga dubu 500 a kowacce rana na man na fitowa ne daga yankin Kudancin kasar.

Kamar yadda Global Witness ta bayyana, kashi 50% na kudaden shigar da kasar ke samu a cikin gida da kuma kashi 93% na kayayyakin da take fitarwa a shekara ta 2009, sun dogara ne kan danyan man da ake hakowa.

Jami'an gwamnatin Sudan sun yi watsi da hasashen da ake yi, cewa tattalin arzikin Arewacin kasar zai durkushe, idan yankin Kudancin ya balle.

Nafie Ali Nafie, wani na hannun damar shugaba Omar al-Bashir, ya ce masu wannan tunani na shashashai ne.

Ya ce ballewar kudancin Sudan ba za ta yi "illa" ga tattalin arzikin Arewacin Sudan, wanda ke da "zabi ta fuskar noma da kuma albarkatun kasa ba".

Suma jama'ar Kudancin na fuskantar matsala, ganin cewa sun dogara ne da man da ake hakowa, wanda kuma zai iya kafewa, abin da ka iya janyo durkushewar yankin ba ki daya.

Karin bayani