Gwamnatin Gbagbo ta kori jakadun burtaniya da Canada

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast
Image caption Gwamnatin Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ta kori jakadun kasashen Burtaniya da kuma Canada daga cikin kasar

Gwamnatin Shugaba Laurent Gbagbo a Ivory Coast , ta kori jakadun Burtaniya da kuma Canada daga kasar .

Kakakin gwamnatin jihar ya ce a makon da ya gabata kasashen biyu suka janye takardun jakadun Ivory coast dake biranen su.

Burtaniya da Canada sunce zasu amince ne kawai da bayanai da suka fito daga wurin Allasane Outtarra, mutumin da kasashen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Sai dai Ba Coulibaly wanda malami ne a kasar, ya ce matakin sanyawa Mr Gbagbo takunkumin ba zai tayar masa da hankali ba

Ya ce baya ganin takunkumin zai yi wani tasiri akan shugabanin siyasar nahiyar Afrika.

Ya kara da cewar da dama daga cikin su, basu damu da yin tafiya zuwa kasashen wajen ba, da kuma ko kasashen duniya ba su amince da su ba.