An fara samun sakamakon zaben gwamna a Delta

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC ta fitarda sakamakon zaben gwamnan jahar Delta na kananan hukumomi guda 20 cikin 25 dake fadin jahar

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC ta fara bayyana sakamakon zaben gwamnan jahar Delta da aka gudanar a jiya.

Ya zuwa yanzu dai Hukumar ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi guda ashirin cikin kananan hukumomi guda ashirin da biyar a fadin kasar.

Ana kuma cigaba da jiran sakamakon zaben jihar Deltan me arzikin mai .

Wata kotu ce ta soke zaben gwamnan jihar wanda aka gudanar a shekerar 2007 bisa dalilin rashin inganci.

Mutumin da ya lashe zaben a wancan lokacin, Emmanuel Uduaghan daga jamiyyar PDP me mulki ya sake tsayawa takarar neman mukamin gwamnan jihar.

An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, kuma a girka jamian tsaron sosai a jihar.

Idan an jima a yau ne za'a fitar da sakamakon zaben