Kamfe din karshe a Kudancin Sudan

kamfe din karshe a Kudancin Sudan
Image caption Wasu daga cikin mahalla kamfe din da aka shirya a Juba na Kudancin Sudan

Ana gudanar da kamfe din karshe a babban birnin Kudancin Sudan, Juba, kafin kuri'ar neman 'yancin kai daga Arewacin kasar, wacce za a gudanar ranar Lahadi.

Wakilin BBC a Juba Peter Martell, ya ce mutane suna cikin murna sosai, yayin da daruruwa suka fito kan tituna domin shiga gangamin.

Za a kuma a gudanar da bikin kade-kade da raye-raye inda makada za su taru domin murnar kuri'ar raba gardamar.

Wannan dai wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2005 domin kawo karshen yakin basasa tsakanin Kudunci da Arewacin kasar.

Jakadan Amurka a Sudan Scott Gration, ya shaida wa BBC cewa yana fatan za a gudanar kuri'ar cikin nasara.

Yace duka bangarorin biyu sun yi alkawarin ganin abubuwa sun tafi kamar yadda aka tsara.

Ya kara da cewa 'yan Kudancin kasar sun bai wa shugaba Bashir tabbacin cewa, ba za su goyi bayan 'yan tawayen yankin Dafur ba.

Karin bayani