Ballewar Sudan ta Kudu: Tambayoyi da amsa

Hakkin mallakar hoto AP

Kusan kashi 99 cikin dari ne na mutane miliyan hudu da suka kada kuri'a a zaben raba-gardamar da aka shirya a watan Janairu ne suka nemi ballewa daga Sudan.

Zaben na daya daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2005, domin samarda zaman lafiya a kasar da ta yi fama da yaki na kusan shekaru 20 tsakanin yankin arewa da kudu.

Me yasa 'yan kudu ke son tasu kasar?

Kamar sauran kasashen Afrika, Turawan mulkin mallaka ne suka tsara iyakar kasar Sudan ba tare da la'akari da babancin kabilu da kuma al'adun kasar ba.

Kudancin Sudan na cike ne da daji da kuma fadama, a yayinda kuma arewacin kasar ke cike da sahara.

Yawancin mazauna arewacin kasar na magana ne da harshen Larabci kuma yawancisu musulmai ne, shi kuma yankin kudancin kasar na tattare ne da kabilu daban-daban wanda yawancinsu mabiya addinin kirista ne da kuma mabiya addinin gargajiya.

A yayin da gwamnatin kasar ke arewaci, wasu mazauna kudu da dama na korafin cewa ana nuna musu banbanci.

'Yan kudancin kasar kuma sun fusata da kokarin gwamnatin kasar na aiwatar da shari'ar addinin musulunci a kasar baki daya.

Me zai faru a gaba?

Sakamakon samun yawan kuri'ar da suka amince da a raba kasar gida biyu, yankin kudancin kasar zai zamo kasa mai cin gashin kai a ranar 9 ga watan Yuli na shekarar 2011 - shekaru shida kenan bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasar.

Image caption Taswirar kudancin Sudan

Kudancin Sudan a shirye yake ya samu 'yancin kai kuwa?

Bayan shekaru da dama na yake-yake a kasar, kudancin Sudan wanda ya fi girman Faransa da Jamus a hade, ba shi da ababen more rayuwa, kamar su hanyoyi da cibiyoyin kiwon lafiya, kuma yankin na da yawan al'ummar da suka kai miliyan takwas.

Shugaban kungiyar tawaye na SPLM ne ke jagorancin yankin tun shekarar 2005, kuma ana ganin ya dan samu kwarewar shugabanci.

Yankin ya samu koma baya ta hanyar samun kudaden shiga daga rijiyoyin mai a yankin, amma masu lura da al'ummura na ganin cewa yankin ya yi amfani da kudin ne wajen inganta sojin sa, a maimakon inganta rayuwar al'ummar yankin.

Gwamnatin yankin kudancin Sudan dai ta tsara jadawalin inganta biranenta da kuma hada sabon taken kasar yankin. Kudancin kasar ya zuwa yanzu na amfani da nasa tutar.

Me zai faru da arewacin kasar?

Abinda gwamnatin arewacin kasar za ta fi mayar da hankali akai shi ne rike kudaden shiga da ake samu ta hanyar sayar da danyen mai, a yayinda kuma yawancin rijiyoyin mai da ke kasar na kudanci ne.

Akwai wata takkadama kan yankin Abiye mai arzikin man fetur, kuma yankin zai kada nasa kuri'ar ne a wani lokacin daban kan wanne bangare yake son hadewa da shi.

Game da yadda rayuwar al'ummar kasar za ta kasance, bangarorin biyu sun amince su bar duk al'ummar kasar su zabi yankin da su ke son su kasance.

Amma Shugaba Bashir ya bada sanarwar aiwatar da shari'ar musulunci a arewacin kasar idan kudanci ya balle, abin da kuma masu lura da al'amura ke ganin zai iya sanya yawancin 'yan kudancin kasar da ke yankin su bar arewacin kasar.

Karin bayani