Shugaba Al Bashir yayi gargadi akan 'yancin kan Kudancin kasar

Shugaba Omar Al Bashir na Sudan
Image caption Shugaban Sudan Omar Al Bashir yayi gargadi akan 'yancin kan Kudancin kasar a nan gaba

Shugaba Omar Al-Bashir na Sudan ya yi garagadin cewa damar da jama'ar kudancin kasar ke da ita a Arewacin kasar zata ragu matukar 'yan Kudancin kasar suka kada kuri'ar amincewa zama kasa mai 'yancin kai a zaben raba gardamar da za'a gudanar ranar lahadi.

Shugaba Albashir ya fadawa gidan talibijin na Aljazeera cewa yankin kudancin sudan ya shafe tsawon shekaru yana yaki kuma ba zai iya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ba, ko kuma wadda zata iya biyan bukatun jama'arta .

Wakilin BBC ya ce shugaba Albashir ya ce idan jama'ar kudancin da ke Abiyei suka jefa kuriar da zata bada yankin ga kudancin kasar watakila hakan ya jefa kasar cikin yaki