Sabon rikici a Jos

Jana'iza a Jos
Image caption Jana'iza a Jos

Hukumomi a jihar Filato sun ce mutane hudu sun mutu a wani sabon tashin hankali da ya barke a Jos, babban birnin jihar.

Wannan tashin hankali ya biyo bayan wani farmaki da aka kaiwa wasu mutane ne da aka ce suna kan hanyarsu ta zuwa daurin aure a karamar hukumar Mangu, inda aka hallaka mutane akalla 6.

Gwamnatin Jihar Filaton ta ce sabon rikicin na Jos bashi da nasaba da harin na Mangu. Kakakin gwamnatin Jihar Filato, Dan Manjang, ya ce rikicin na Jos yana da nasaba da zabubbukan da jam'iyyar adawa ta CPC ta gudanar a jihar.

Jami'an jam'iyyar CPC sun musanta wannan ikrari, suna masu cewar laifin kasawar gwamnatin jihar Filato ne. Jam'iyyar ta ce mafita ga lamarin da ake fama da shi a jihar shine a kafa dokar ta baci.