Wani sabon rikici ya tashi a Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na cewa an sami barkewar wani sabon tashin hankali a yau din nan.

Tashin hankalin ya biyo bayan wani farmaki ne kan wasu masu zuwa daurin aure, wadanda suka tashi daga birnin na Jos zuwa garin Mangu dake a cikin jihar ta Filato.

A rikicin na yau dai an yi kone-kone, sannan kuma ya rutsa da mutane, sai dai Yan sanda sun ce babu wanda ya rasa ransa a sakamakon wannan al'amari, amma wasu sunce sun ga gawar mutanen da suka mutu.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da rigingimu na kabilanci da na addini wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane cikin shekaru goma.

To har ila yau kuma wasu rahotannin daga jihar Gombe na cewa wasu 'yan bindiga da ba a tantance ko su wane ne ba, sun bude wuta a kan wasu mutane a Unguwar Federal Low-cost dake garin na Gombe.

Wannan lamari dai ya faru ne jiya da dare kuma wadanda suka sheda lamarin sun ce an sami hasarar rayuka. Sai dai kuma rundunar 'yansandan jihar ta Gombe ta bayyana cewa tana kan biciken al'amarin.