An sace 'yan kasar Faransa biyu a Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba dauke da makamai sunyi awon gaba da wasu Faransawa biyu a jamhuriyar Nijar

Hukumomin kasar Nijar sun tabbatar da harin da wasu mutane dauke da makamai da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gidan abinci a daren jiya inda suka yi awon gaba da wasu turawa 2 'yan kasar Faransa.

A wata hira da manema labarai kakakin gwamnatin kasar Dr Mahaman Lawali Dandah ya ce ya zuwa yanzu jami'an tsaro sun gano yan fashin a yankin arewacin Walam a jahar Tilaberi inda suka yi musu kawanya

Daya daga cikin mutanen dai na shirin auren wata 'yar Nijar a makon gobe.

Kungiyar Al qa'eda a yankin magrib dai ta sha gudanar da jerin sace sacen mutane a jamhuriyar Nijar, sai dai kuma ba'a taba sace 'yan kasashen waje a cikin babban birnin kasar ba.

A 'yan watanni ukun da suka gabata ma, wasu mayakan kungiyar AQMI ko kuma ALQAEDA sun sace wasu haifaffun kasar Faransan su 5 a yankin Agadez na arewacin Niger.