An hallaka wasu Faransawa biyu a Niger

Nicholas Sarkozy
Image caption Nicholas Sarkozy

Ministan harkokin tsaron kasar Faransa, Mr Alain Juppe, ya ce an hallaka wasu Faransawa guda biyu da aka sace a Jamhuriyar Niger.

A jiya ne aka yi awon gaba da Faransawan guda biyu daga wani gidan cin abinci a Niamey babban birnin Niger.

Kamar yadda ministan tsaron na Faransa ya bayyana an hallaka Faransawan guda biyu ne a wani yunkuri na cetosu da aka yi, wanda ya hada da sojojin kasar Faransa.

An gano gawawwakin Faransawan ne, wadanda har zuwa yanzu ba'a bayyana sunayensu ba, akan iyakar da ke tsakanin Niger da Kasar Mali, bayan wani dauki ba dadi da aka yi.

Haka nan kuma sanarwar da ma'aikatar tsaro ta Faransa ta fitar ta ce an hallaka wasu daga cikin 'yan fashin.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace mutanen.