Sabon tashin hankali a Jihar Filato

Rikici a Bukuru

Rahotanni daga Nigeria sun ce ana can ana zaman zullumi a garin Bukur da ke gab da birnin Jos, bayan da wani sabon tashin hankali ya barke.

Kawo yanzu babu wani labari akan adadin mutanen da suka hallaka ko su ka samu raunika a wannan rikici.

Sabon tashin hankalin dai ya barke ne a Unguwar Doki dake garin na Bukur, dake karamar hukumar Jos ta Kudu.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato Abdulrahaman Akano, wanda ya tabbatar da aukuwar wannan rikici, ya ce tashin hankali ya faru ne bayan da jami'an tsaro suka hana wasu mutane daukar fansa bayan da suka yi zargin wasu mutane sun kona musu gida a lokacin da suka yi bulaguro.

Abdulrahaman Akano ya kara da cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin na Bukur domin tabbatar da doka da oda.

Wadanda suka ga abun da ya faru sun ce sun ga an cinna wa gine-gine wuta a garin na Bukur mai nisan kimanin kilomita ar'ba'in daga Jos babban birnin jihar