'Yan Kudancin Sudan sun fara jefa kuri'unsu

Taswirar Kudancin Sudan
Image caption 'Yan gudun hijirar da suka fito daga Kasar Sudan wadanda ke kasar Australia sun fara jefa kuri'unsu dangane da 'yancin kan kudancin Sudan

Jama'ar kudancin kasar Sudan sun fara kada kuri'a a zaben raba gardama kan kasancewar kudancin Sudan a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Shugaban yankin kudancin kasar Salva Kiir ya kada kuri'arsa kuma ya bayyana cewar wannan wata rana ce ta tarihi a garesu

A can kasar Australia ma dubun dubatar 'yan gudun hijirar da suka fito daga kasar ta Sudan sun kada kuri'arsu .

Anyi ta gudanar da kade kade da kuma raye raye a yankin kudancin kasar gabanin lokacin da mutane suka farav kada kuri'unsu.

Wakilin BBC ya ce kuri'ar da za'a jefa, na cikin wani shiri, wanda zai kawo karshen yakin basasa tsakanin Arewacin Sudan da kuma Kudancin kasar, wanda suka shafe tsawon shekarun suna yi, wanda kuma zai kai ga darewar kasar