Zaben raba gardama dangane da Kudancin Sudan

Taswirar Kudancin Sudan
Image caption 'Yan gudun hijirar da suka fito daga Kasar Sudan wadanda ke kasar Australia sun fara jefa kuri'unsu dangane da 'yancin kan kudancin Sudan

Jama'a sun fara kada kuri'a a zaben raba gardama kan kasancewar kudancin Sudan a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Dubun dubatar yan gudun hijirar da suka fito daga kasar ta Sudan sun kada kuri'arsu a kasar Australia .

Idan an jima a yau ne dai za'a bude rumfunan zabe a kasar Sudan.

Wakilin BBC ya ce kuri'ar da za'a jefa, na cikin wani shiri, wanda zai kawo karshen yakin basasa tsakanin Arewacin Sudan da kuma Kudancin kasar, wanda suka shafe tsawon shekarun suna yi, wanda kuma zai kai ga darewar kasar