Ana kada kuru'ar raba gardama a Sudan

Masu kada kuru'a a kudancin Sudan

Jama'a sun fita kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri'a te neman 'yancin kai a yankin kudancin Sudan. Ana sa ran wannnan kuru'ar raba gardama zata sanar da sabuwar kasa a duniya.

Dubun dubatar mutane ne suka yi dogayen layuka a rumfunan zabe kafin ma a fara kada kuri'ar.

Daga cikin wadanda suka fara kada kuri'a har da shugaban yankin kudancin na Sudan Salva Kiir.

'Yan yankin kudancin Sudan din dake zaune a arewacin kasar suma zasu kada kuri'a, sai dai rahotanni sun ce ana kada kuri'ar ne sannu-sannu.