Amurka na tuhumar wani saurayi da laifin kisa

Gabrielle Giffords, 'yar majalisar Amurka

Masu shigar da kara na gwamnatin tarayyar Amurka sun tuhumi wani mutum mai shekaru ashirin da biyu da laifin harbin 'yar majalisar wakilai, Gabrielle Giffords a ranar Asabar a jihar Arizona.

Ana tuhumar Jared Loughner ne da laifin kisan mai sharia John Roll da daya daga cikin mukarraban Gifford, da kuma yunkurin kisan wasu mutanen biyu da kuma ita kanta 'yar majalisar.

Mutane shida ne dai suka rasu lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta yayin da Ms Giffords ke ganawa da 'yan mazabarta a garin Tucson.

Likitocin da ke jiyyar 'yar majalisar da aka harba a ka sun ce su na sa ran za ta iya warkewa sarai.