Brazil ta yi gargadi kan yakin kasuwanci

Ministan Kudin Brazil, Guido Mantega
Image caption Brazil ta yi gargadi kan afkuwar yakin takardun kudi

Brazil ta yi gargadin cewa duniya na fuskantar barazanar afkawa yakin kasuwanci sanadiyyar abin da ta kira sauya darajar kudade da gangan da kasashen duniya ke yi.

Ministan kudin Brazil, Guido Mantega ya shaidawa jaridar Financial Times cewa, Brazil na daukar matakan da za su hana karuwar darajar kudinta, kuma za ta tada batun badakalar darajar kudaden a taron kungiyar ciniki ta duniya da kuma kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki.

Mista Mantega ya ce, yakin takardun kudade na neman komawa yakin kasuwanci.

A baya-bayan nan dai kasashen duniya, musamman masu tasowa na korafi kan yadda kasashen da suka ci gaba ke karya darajar takardun kudinsu domin samun bunkasar tattalin arzikinsu.