Kungiyar ETA za ta tsagaita buda wuta a Spain

Wasu 'yan kungiyar ETA
Image caption Wasu 'yan kungiyar ETA

Kungiyar 'yan aware ta Basque, wato ETA, ta bada sanarwar dakatar da bude wuta na din-din-din a fadan da take na kawo karshen shugabancin da Spain ke yiwa yankin Basque.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a wata jarida dake da kusanci da kungiyar, ETA ta ce za ta aiwatar da dakatar da bude wuta na din-din-din, wanda kasashen duniya za su yi na'am da shi.

Sai dai kuma duk da wannan sanarwar, gwamnatin Spain ta bakin ministan cikin gidanta, ta ce har yanzu kungiyar ta ETA ta gaza kawo karshen tashe tashen hankula da take a yankin.