Goodluck da Atiku sun yi nasara a kotu a kan takara

Atiku Abubakar
Image caption Yanzu saura siradin tantancewa

Dazu ne wata kotu a Abuja ta kori karar da wasu suka shigar, suna neman a hana shugaba Goodlukc Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a bana.

Har ila yau kotun ta kori wasu kararraki biyu da wasu suka shigar, suna neman a hana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsayawa takarar shugaban kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Wasu magoya bayan wadannan bangarori biyu ne dai suka shigar da wannan kara.

Hakan na zuwa ne a daidai a jajibirin soma tantance masu neman tsayawa jami'iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben badi.

Wadanda suka kai Ahugaba Goodluck kara sun ce tsayawarsa zabe ta keta yarjejeniyar karba-karba ta jam'iyyar.

Su kuma wadanda suka kai Atiku Abubakar kara sun ce yana da wasu tuhume-tuhume a kansa.