Ministan tsaron Faransa ya kai ziyara Nijar

Tutar kasar Nijar
Image caption An gargadi masu yawon bude ido su kaurace

Ministan tsaron kasar Faransa, Alain Juppe, ya dora alhakin mutuwar wasu Faransawa biyu da aka sace a birnin Yamai na Nijar a kan wadanda suka yi garkuwa da su.

Mista Juppe ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar da ya kai yau a Nijar din, inda ya gana da shugaban mulkin sojan kasar, Janar Salou Djibo, da kuma kungiyar Faransawa mazauna Nijar.

Ministan tsaron Faransar ya kuma ce, sojan Faransa ba su da hannu a mutuwar wasu jami'an tsaron Nijar ukku na jandarma, wadanda suka hallaka a farmakin neman kubutar da 'yan Faransar biyu.

Sannan yayi kira ga 'yan yawon shakatawa Faransawa da su kauracewa Nijar.