Dan majalisar Amurka ya nufi gidan-yari

Tom Delay
Image caption An yankewa Tom Delay hukunci

An yankewa tsohon jagoran jam'iyyar Republicans ta Amurka Tom Delay hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa rawar da ya taka wajen raba kudaden haram ga 'yan takarar cikin jam'iyyarsa.

Haka kuma an yi masa daurin je-ka ka gyara halinka na shekaru goma bisa laifin halatta kudin haram.

A watan Nuwamba ne aka samu Mista DeLay da laifin raba gudunmawar kamfanoni ga 'yan takarar jam'iyyar Republican a jihar Texas a shekarar 2002.

Bayan da aka tuhume shi dai, ya sauka daga mukaminsa na shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Amurka kafin daga bisani ya bar siyasa dungurungum.