Garin Jos ya zama fayau bayan rikici

Babban birnin jihar Filato a Najeriya, wato Jos, ya zama fayau bayan rikice-rikicen addini da na kabilanci wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha takwas.

Wani dan jarida a garin na Jos, Andrew Agbese, ya shaidawa BBC cewa bankuna da makarantu da kuma kasuwanni sun kasance a rufe saboda fargabar tashin hankali.

An yi kone-konen gidaje a wasu sassan jihar, amma dai an turra jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Jos dai ta na yankin tsakiyar Najeriya ne, inda Kirista da Musulmi ke fada da juna, saboda dalilai na addini da kabilanci da kuma neman madafun iko a garin.

Jihar dai ta yi fama da rikici na tsawon shekaru goma, inda aka yi mummunan rikici a shekarun 2001 da 2008 da kuma bara.

"Babu jama'a a garin, duk sun watse; hatta kasuwanni da ya kamata a ce ana hadada sun zama fayau, saboda shaguna sun kasance a rufe." In ji Mr Agbese a hirarsa da BBC.

"Ya kamata a fara karatu a jami'a, amma hakan bai yiwu ba, saboda dalibai su na cikin fargaba."

Harin bas din daurin aure

Ya ce an fara rikicin ne bayan da aka kaiwa wata motar bas hari, inda aka kashe musulmi a lokacin da su ke dawowa daga daurin aure a yammacin ranar Juma'a.

Matasa musulmi sun gudanar da zanga-zanga domin nuna bakin cikin su da mutuwar mutane bakwai a harin.

'Yan sanda sun ce mutane goma sha daya ne suka mutu bayan zanga-zangar da aka gudanar ranar Asabar, abin da mahukunta a jihar ke alakantawa da taron siyasa da jam'iyyar CPC ta gudanar.

Image caption Taswirar Najeriya

An gurfanar da 'yan siyasa bakwai 'yan jam'iyyar CPC a gaban kotu, bayan an tuhume su da tayar da rikicin.

An kuma sake kama mutane hudu bayan rikicin da ya biyo baya a Bukuru a ranar Lahadi, inda aka ce an ga gawarwaki bakwai.

A ranar Litinin ma, an yi ta guje-guje a Anglo-Jos wanda ya ke wajen garin Jos: Musulmi da Kirista ne ke zaune a yankin.

Sojoji da 'yan sanda na ci gaba da sintiri a manyan hanyoyi a garin na Jos domin tabbatar da tsaro.

A bara, malaman addini a Najeriya sun zargi 'yan siyasa da haddasa fitina a garin na Jos.

Kusan mutane tamanin ne suka mutu a lokacin da bama-bamai suka tashi ranar jajibirin Kirsimeti, abin da kuma ya janyo rikici washegarin ranar.

A safiyar ranar Talata ma wani rikicin da ya sake barkewa a Jos ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane goma sha uku.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya ce sun tura jami'ansu zuwa wani kauye na mabiya addinin Kirista a yankin Wareng bayan harin da aka kai.

Wasu mazauna kauyen sun ce sun ga gawarwakin mutane goma sha uku wadanda ke dauke da raunukan da aka ji musu da adduna da bindigogi.

'Yan sanda sun ce a cikin kwanaki ukun da suka wuce sama da mutane talatin ne aka kashe a fadan kabilanci da addini da ake yi a garin na Jos.