Majalisar dinkin duniya ta soki Ivory Coast

Babban zauren majalisar dinkin duniya
Image caption Majalisar dinkin duniya ta soki Ivory Coast

Majalisar dinkin duniya ta yi suka kan amfani da kafafen yada labarai a Ivory Coast domin yada abin da ta kira bayanan karya da kuma iza wutar kiyayya da tashin hankali.

A wata sanarwa da shugabar kwamitin tsaro na majalisar kuma mataimakiyar jakadar Bosnia a majalisar Mirsada Colakovic ta bayar, ta yi tur da yadda kafafen yada labaran ke zuga kan a yiwa jami'an majalisar bore.

Ta ce: ''Wakilan kwamitin tsaro na majalisar na kakkausar suka tare da bukatar dakatarwa nan take ga amfani da kafafen yada labarai musamman ma RTI wurin yada karairayi, da rura wutar gaba da tashin hankali har a kan jami'an majalisa''.

Mutane da dama ne dai aka kashe a Ivory Coast din, sanadiyyar rikicin da ya biyo bayan zaben shugabancin kasar na watan Nuwamba mai cike da rudani.