Jonathan da Atiku sun tsallake tantancewar PDP

Jami'ayar ta PDP mai mulki a Najeriya ta amincewa Shugaba Goodluck Jonathan da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma Sarah Jubril tsayawa takarar zaben fidda gwani na takarar Shugaban kasa a inuwarta.

Jama'iyar ta amince da mutanen ukku ne bayan da suka halarci zaman tantancewar da ta shirya yau a hedikwatarta dake a Abuja.

Tun farko dai an sa ran cewa, mutane hudu ne za su bayyana a gaban kwamitin tantance 'yan takarar, saidai mutum na hudun , Alhaji Aminu Dutsinma ya ce bai ga dalilin da zai sa ya halarci taron ba saboda ba ya kan ka'ida domin a cewarsa kotu ta yanke hukuncin cewar akwai batun zagaya iko tsakanin sassan kasar, don haka bai kamata Yan Arewa su bayyana a tantancewar tare da Shugaba Goodluck Jonathan,wanda ya fito daga kudancin kasar ba.

Tun kafin fara tantance 'yan takarar, bangaren Atiku Abubakar sun nuna rashin gamsuwa da wasu daga cikin wakilan kwamitin , suna nuna shakku kan ko zasu nuna adalci a aikin nasu, sai dai Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba wannan kwamitin ne suka nuna rashin gamsuwa da shi ba, illa wanda zai shirya babban taron jama'iyar na kasa, inda za a fitar da dan takarar Shugaban kasa na Jama'iyar.